Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Maye gurbin Riek Machar ya sabawa yarjejeniyar zaman lafiya

Majalisar Dinkin Duniya ta gargadi shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Kiir kan maye gurbin mataimakin sa Riek Machar da yayi wanda tace ya sabawa yarjejeniyar zaman lafiyar kasar.

Shugaba Salva Kiir da sabon mataimakinsa Taban Deng Gai a fadar shugaban kasar dake birnin Juba
Shugaba Salva Kiir da sabon mataimakinsa Taban Deng Gai a fadar shugaban kasar dake birnin Juba REUTERS/Jok Solomun
Talla

Kakakin Majalisar Farhan Haq yace duk wani nadi da za’ayi sai ya dace da yarjejeniyar da aka kulla, wanda hakan ke nuna adawa da nadin Tabal Den Gai a matsayin sabon mataimakin shugaban kasa

Tun dai lokacin da sabon rikicin kasar ya barke ne, Mr. Machar ya fice daga birnin Juba bayan ya yi zargin cewa shugaba Salva Kiir na shirin kashe shi.

Gabanin daukan matakin sauya shi, sai da Salva Kiir ya bai wa Riek Machar wa’adin sa’oi 48 da ya dawo Juba ko kuma ya maye gurbin shi.

Sabon rikicin da ya barke bayan dawowar Riek Machar kasar a matsayin mataimakin shugaban kasar ya hallaka mutane sama da dari biyu a rikicin kwanaki hudu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.