Africa
Kungiyar Boko Haram ta samu sabon shugaba
Kungiyar masu tada kayar baya ta IS ta bayyana Abu Musab al-Barnawi a matsayin sabon jogaran reshenta da ke yammacin Afirka wato Boko Haram.
Wallafawa ranar:
Talla
A baya Abu Musab al-Barnawi ya kasance mai Magana da yawun kungiyar ta Boko Haram kafin sanar da bashi wannan matsayi.
Sai dai kuma yayin da IS ke sanar da canjin sabon shugabancin, kungiyar ba ta ce komai ba dangane da tsohon jagoran kungiyar ta Boko Haram Abubakar Shekau.
Tun a watan Agustan da ya gabata ne aka ji muryar Shekau a wani sakon murya da aka watsa a internet inda yake cewa har yanzu yana nan a raye.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu