Isa ga babban shafi
Najeriya

An gano Sojojin Najeriya 5 da suka bata

Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da gano wasu daga cikin sojojinta da suka bata a wata arangama da suka yi da mayakan Boko Haram a kauyen Guro Gongon cikin jihar Borno.

Kanal Usman Kukasheka Kakakin rundunar Sojin Najeriya
Kanal Usman Kukasheka Kakakin rundunar Sojin Najeriya via twitter
Talla

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar Sojin ya fitar, Kanal Usman kukasheka ya ce an sake gano Sojojin guda biyar a wani aikin bincikensu da rundunar sojin ta kaddamar.

Sai dai bai fadi adadin Sojojin da suka bata ba a lokacin arangamar da dakarun suka yi da ‘Yan Boko Haram a ranar 20 ga watan Yuli a kauyen na Guro Gongon.

Sojoji kimanin 19 ne dai suka samu munanan rauni a arangamar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.