Isa ga babban shafi
Burundi

MDD na nazari kan tura dakaru dubu 3 Burundi

Ganin yadda al’amura ke ci gaba da tabarbarewa a kasar Burundi, sakatare janar na majalisar dinkin duniya Ban Ki Moon, na nazari kan irin rawar da ‘yan sanda 3,000 za su taka don aikin samar da zaman lafiya a cikin kasar.

Sakatare Janar na Majalisar dinkin duniya Ban Ki-moon.
Sakatare Janar na Majalisar dinkin duniya Ban Ki-moon. Reuters
Talla

Majalisar na ci gaba da fuskantar matsin lamba ganin yadda ake ci gaba da kai hari kan fararen hula da kuma masu adawa da gwamnatin shugaba Pierre Nkurunziza.

Mr. Ban ya ce, aika dakaru dubu 3, shi ne matakin da zai kare lafiyar al’ummar Burundi.

To sai dai Nkurunziza ya dade yana adawa da shirin tura jami’an tsaro zuwa kasar wadda ta fada cikin rikici tun bayan da ya sanar da shirinsa na neman wa’adi na uku a karagar mulki kuma tuni ya lashe zaben da aka yi.

Rikicin siyasar Burundi dai ya hallaka mutane fiye da 400 tare da tilasta wa dubu 250 kauracewa kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.