Isa ga babban shafi
Burundi

Ban Ki Moon zai gana da Nkurunziza

Akalla mutane hudu ne suka rasa rayukansu a wani sabon rikici da ya barke a kasar Burundi, al’amarin da ke zuwa a dai dai lokacin da Sakatare janar na majalisar dinkin duniya Ban Ki-Moon ya soma ziyara a Bujumbura babban birnin kasar.

Ban ki Moon Sakatare Janar na majalisar Dinkin Duniya da sauka kasar Burundi
Ban ki Moon Sakatare Janar na majalisar Dinkin Duniya da sauka kasar Burundi © Griff Tapper / AFP
Talla

A karon farko kenan tun bayan da Burundi ta tsunduma cikin tashin hankali a watan Afrilun bara, da Sakatare janar na majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Mon ya kai ziyara babban birnin Bujumbura na kasar.
Ana sa ran a yau Talata Mista Ban ya gana da shugaba Pierre Nkurunziza bayan ganawarsa da shugabannin jam’iyyun siyasa da kungiyoyin fararen hula, a wani mataki na kokarin warware rikicin watanni 10 da kasar ke fama da shi.

Bayan kammala ziyara tasa a Burundi, ana sa ran Mista Ban zai isa Jamhuriyar Demokradiyar Congo kafin daga bisani ya leka kasar Sudan ta kudu , inda yakin basasa ya barke a watan Disamban shekara ta 2013.
Bayan wasu ‘yan sa’oi da isarsa Burundi a yammacin jiya litinin, wasu hare haren gurneti guda biyu suka yi sanadin ajalin akalla mutane biyu tare da jikkata tara.

Tuni dai hukumomin kasar suka bayyana farmakin a matsayin aikin ta’addanci.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.