Isa ga babban shafi
Burundi

Za a bincike sojojin Burundi saboda cin zarafi

Majalisar dinkin duniya za ta tasa keyar wasu sojojin Burundi da ke aiki a Jamhriyar Afrika ta Tsakiya zuwa kasarsu ta asali, domin fuskantar tuhuma akan zargin da ake yi musu na hannu a cin zarafin kananan yara mata a Afrika ta tsakiya mai fama da rikici. 

Ana zargin sojojin Buruni da hannu a laifin cin zarafin kananan yara mata a Afrika Tsakiya
Ana zargin sojojin Buruni da hannu a laifin cin zarafin kananan yara mata a Afrika Tsakiya RFI
Talla

Wata majiyar majalisar a birnin Bangui ta ce, nan da ‘yan kwanaki masu zuwa za a tasa keyar Pierre Niyonzima da Jimmy Rushehse da kuma Jean Mushimantwari da ke sa ido kan aikin soji a Afrika ta Tsakiya .

Majalisar dinikin duniya ta ce, ta samu bayanai da ke nuna cewa sojojin sun keta hakkin bil’adama, kuma tuni aka sanar da hukmomin Burundi akan wannan shirin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.