Isa ga babban shafi
Burundi

Amurka na zargin Rwanda da hannu a rikicin Burundi

Kasar Amurka ta zargi Rwanda da hannu cikin tahsin hankalin a ake samu a kasar Burundi wanda ya kunshi hayar 'yan gudun hijira domin kai hari kan gwamnatin kasar.

Kasar Burundi na fama da tashe tashen hankula
Kasar Burundi na fama da tashe tashen hankula REUTERS/Goran Tomasevic/Files
Talla

Jakadan Amurka a yankin, Thomas Perrielo ya ce su na da shaidun da ke nuna cewar Rwanda na hayar 'yan gudun hijirar don kai hari Burundi.

Wannan shi ne karo na farko da Amurka ke fitowa karara ta zargi Rwanda kan tashin hankalin da ake samu a Burundi.

Ita ma Burundi ta dade ta na zargin cewa da sa hannun Rwanda a rikcin da ta ke fama da shi wanda ya barke  tun lokacin da shugaban kasar Pierre Nkunrunzia ya sanar da aniyarsa ta neman wa’adin shugabanci karo na uku.

Rikicin Burundi ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama yayin da shugaban kasar ya yi watsi da bukatar kungiyar tarayyar Afrika na tura dakaru domin samar da zaman lafiya a kasarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.