Isa ga babban shafi
Burundi

AU ta isa Burundi don sasanta rikicin kasar

Wata tawagar kungiyar Tarayyar Afirka ta isa birnin Bujumbura na kasar Burundi a yau Alhamis domin ganawa da hukumomi da kuma ‘yan adawa na kasar, kwanaki biyu bayan da babban magatakarda na Majalisar dinkin duniya Ban Ki-Moon ya ziyarci kasar.

Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza
Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza REUTERS/Evrard Ngendakumana
Talla

Tawagar dai ta kunshi shugabannin kasashen Sengal da Afirka ta kudu da Gabon da Mauritania da kuma Firaministan Habasha, inda za su yi kokarin shawo kan shugaba Pierre Nkurunziza domin shiga tattaunawa da ‘yan adawa da nufin kawo karshen rikicin siyasar kasar na watanni 10.

Kasar Burundi ta tsindima cikin rikici ne tun bayan da Nkurunziza ya sanar da aniyarsa ta sake tsayawa takara domin neman wa’adi na uku akan karagar mulki, al’amarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 400.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.