Isa ga babban shafi
Burundi

Ban Kin Moon ya soma ziyara a Burundi

A wani lokaci a yau ne, babban magatakarda na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon zai isa a birnin Bujunbura na kasar Burundi domin ganawa da hukumomi da kuma ‘yan adawa na kasar.

Babban Magatakarda na MDD, Ban Ki-moon.
Babban Magatakarda na MDD, Ban Ki-moon. REUTERS/Adrees Latif
Talla

An dai tsara Ban Ki-moon zai gana da shugaba Pierre Nkurunziza, da kuma shugabannin jam’iyyun adawa na kasar don ganin an kawo karshen tashe tashen hankula a kasar.

Ko a yau litinin dai an kai wani harin ban a birnin Bujumbura tare da kashe mutum daya da kuma raunata wasu 7.

Burundi na ci gaba da fama da rikice-rikice tun bayan da shugaba Pierre Nkuruziza ya yi yunkurin sake tsayawa takara har zuwa wannan lokacin da ya kuma ci gaba da mulki bayan lashe zaben kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.