Isa ga babban shafi
Burundi

Burundi : Nkurunziza ya amince ya shiga tattaunawar sulhu

Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza ya amince ya shiga tattaunawar sulhu domin kawo karshen rikicin kasar da aka shafe tsawon watanni 10 ana kashin mutane. Sai dai bangaren ‘Yan adawa sun yi watsi da matakin.

Shugaban Burundi Pierre Nkurunziza tare da Ban Ki-moon a Bujumbura
Shugaban Burundi Pierre Nkurunziza tare da Ban Ki-moon a Bujumbura REUTERS/Evrard Ngendakumana
Talla

Shugaba Pierre Nkurunziza ya amince da matakin tattaunawar ne bayan ganawa da Babban Magakatarda na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon wanda ya ziyarci kasar.

Ban yace dukkanin bangarorin biyu sun amince su hau teburin sulhu domin kawo karshen rikicin kasar da ke dab da jefa ta cikin yakin basasa.

Tun a jiya Litinin ne Ban Ki-moon ya isa birnin Bujunbura, domin ya gana da shugaba Nkurunziza da kuma wakilan ‘yan adawa, a kokarin samar da mafita ga rikicin siyasar kasar wanda ya samo asali daga canza kundin tsarin mulki da aka yi cikin shekarar da ta gabata.

Sai dai mai magana da yawun ‘yan adawar Charles Nditije, ya ce a yanzu sun zura ido ne domin ganin cewa shugaba Nkurinziza ya mutunta kalaman da ya yi a gaban Ban Ki-oon.

Nditije ya bayyana shakku akan ko Nkurunziza zai mutunta irin kalaman da ya furta musamman game da yin sulhu da abokannin hamayyarsa bayan ganawarsa ta Banki-Moon.

Ya kara da cewa, ya kamata duniya ta fahinci cewa matukar Nkurunziza ya ki amincewa da kokarin da kasashen duniya ke yi wajen samar da zaman lafiya a kasar, to dole ne Majalisar Dinkin Duniya ta shiga cikin wannan batu domin kare al’umma daga salon mulkin Nkurunziza.

To sai dai ministan harkokin wajen Burundi Alain Aimé Nyamitwe, ya ce fatansu zaman lafiya a kasar, amma ba za su taba amincewa da take-taken wadanda ke tayar da rigima a kasa ba.

Sama da mutane 400 suka mutu, yayin da sama da dubu dari biyu da arba’in suka fice daga kasar saboda tsoron barkewar yakin basasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.