Isa ga babban shafi
Togo

Ba'amurke ya kamu da zazzabin Lassa a Togo

Wani likita Ba’amurke da ya kamu da zazzabin Lassa a wata kasa ta yammacin Afirka, zai samu kulawa a wani kebabben wuri na kula da masu fama da cututukan da ke saurin yaduwa a jihar Atlanta da ke Amurka.

Nau'in beran da ke haifar da cutar zazzabin Lassa
Nau'in beran da ke haifar da cutar zazzabin Lassa wikimedia
Talla

A jiya ranar juma’ar da ta gabata ne aka dauki Ba’amurken a cikin wani jirgin likita daga kasar Togo zuwa gida kamar dai yadda hukumomi suka tabbatar.

Masani kiwon lafiya sun bayyana Lassa a matsayin cutar da ke haddasa zubar jini a cikin jikin dan adam, kuma alamu da yadda take yaduwa ba su da bambanci da irin na cutar Ebola.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.