Isa ga babban shafi
Cote d'ivoire

An kamala shara'ar kisan Janar Guei a Cote d'Ivoire

A Cote D’ivoire wata kotun sojin kasar ta zartas da hukunci daurin rai da rai zuwa wasu tsoffin sojan kasar dake da hannu a kisan tsohon Shugaban sojin kasar Janar Robert Guei.

Tsohon Kwamadan sojan kasar Anselme Seka Yapo a zaman kotun
Tsohon Kwamadan sojan kasar Anselme Seka Yapo a zaman kotun SIA KAMBOU / AFP
Talla

Kotun ta yanke hukuncin dauri rai da rai zuwa wasu sojojin uku dake da hannu a kisan tsohon Shugaban sojin kasar Janar Robert Guei a shekara ta 2002.
An dai kwashe tsawon wata daya ana gudanar da wannan shara’ar,
Mutane uku sun hada da tsohon kwamandan soja Anselme Seka Yapo,tsohon dogari matar tsohon Shugaban kasar Simone Gbagbo,wani janar din sojin mai suna Brunot Dogbo Ble da wani soja mai mukamin Sajen Daleba Sery.
Kotun bayan ta saurari wasu mutane 19 da ake tuhuma da hanu a wanan kisa,ta kuma zartas da hukunci daurin shekaru 10 yayinda ta salami wasu mutanen a daya wajen.

Tsohon Shugaban kasar da aka halaka janar Robert Guei ya na mai shekaru 61 da kuma aka kashe ranar 19 ga watan satumba na shekara ta 2002 bayan da yayi kokarin kiffar da gwamnatin shugaban kasar na lokacin Laurent Gbagbo,wanda ya lashe zaben kasar na shekara ta 2000 a kasar ta Cote D’ivoire.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.