MDD
MDD zata rage yawan dakarun wanzar da zaman lafiya a Cote D'Ivoire
Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya tsaida shawaran rage yawan sojan wanzar da zaman lafiya da ake dasu a kasar Cote D’Ivoire, inda ake fama da yakin basasa na tsawon shekaru 5 da suka gabata.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Talla
Wakilan majalisar su 15 ne suka amince da rage yawan Dakarun, 4,000 daga cikin 5,437 tun daga watan jibi, na Maris.
Matakin na zuwa ne bayan kasar ta yi nasarar gudanar da zabe sahihi da ya sake baiwa Shugaban kasar Alassane Ouattara damar lashe zaben mulkin kasar na tsawon shekaru 5.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu