Isa ga babban shafi
Cote d'Ivoire

Rikicin siyasar Cote D'Ivoire; Ble Goudel a gaban Kotun Duniya

Jagoran matasa magoya bayan tsohon shugaban Cote D’Ivoire wanda yanzu haka ke hannun Kotun Duniya da ke Hague Laurent Bagbo wato Charles Ble Goude, na a gaban kotun ta duniya a wannan litinin domin yi masa shari’a dangane da rawar da ake zargin ya taka a rikicin da ya biye bayan zaben shugabancin kasar na shekara ta 2010.

Na hannun damar Laurent Bagbo, Charles Ble Goude
Na hannun damar Laurent Bagbo, Charles Ble Goude
Talla

Za a dai share tsawon kwanaki 4 ana gudanar da wannan shari’a, kuma wasu daga cikin zarge-zargen da ake yi masa sun hada da aikata kisan kare dange da kuma tunzura jama’a domin tayar da fitini a cikin kasar da ke Yammacin Afirka.

Kotun dai na zargin Ble Goude da kuma Bagbo da kasancewa ummulhaba’isin tashin rikice-rikicen da suka barke daga ranar 16 ga watan disambar shekara ta 2010 zuwa 12 ga watan Afrilun shekara ta 2011 tare da haddasa asarar rayukan mutane akalla dubu uku a kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.