Cote d'Ivoire
MDD ta nuna damuwarta kan harin da magoya bayan Gbagbo ke shirin kaiwa
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwar ta kan shirin magoya bayan tsohon shugaban kasar Cote d’Ivoire, Laurent Gbagbo, na kaddamar da hare hare cikin kasar da taimakon ‘Yan tawayen Liberia.
Wallafawa ranar:
Talla
Magoya bayan tsohon shugaban sun dade suna ta da hankali, tun bayan da aka kauda shugaban nasu daga karagar mulki, abinda ya baiwa Alassane Ouattara da ya lashe zabe damar jagorancin kasar.
A ‘yan watannin nan an tura dakarun kasar tare da na Majalisar Dinkin Duniya zuwa kan iyaka bayan wasu hare hare da aka kai akan wasu kauyuka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu