Isa ga babban shafi
Mali

An kafa dokar ta baci ta kwanaki 10 a Mali

Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita ya sanar da kafa dokar ta-baci ta tsawon kwanaki 10, tare da zaman makoki na kwanaki uku bayan garkuwa da mutane da wasu ‘yan bindiga suka yi a wani otel da ke birnin Bamako, lamarin da a hukumance aka ce ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 21.

Dakarun kasar Mali a Otel Radisson na Birnin Bamako
Dakarun kasar Mali a Otel Radisson na Birnin Bamako AFP PHOTO / HABIBOU KOUYATE
Talla

Majiyoyin tsaro sun ce daga cikin wadanda suka rasa rayukansu akwai Ba’amurke daya,yan kasar Rasha shida da dan kasar Belgium daya da kuma wasu China uku.

Jami’an tsaron kasar Mali da kuma na kasashen ketare da suka hada da Faransa da Amurka, sun share tsawon yinin juma’a kafin ceto mutane 170 da aka yi garkuwa da su a Otel Radisson da ke birnin na Bamako.

A yau asabar Shugaban kasar Mali ya samu isowa Otel din domin ganewa idanu sa ta'asar da yan ta'ada suka aikata.

Shugaban Rasha Vladmir Poutine ya aike da sako zuwa Shugaban Mali  na cewa kasar sa za ta bayar da gudumunwa wajen yaki da ta'adanci.

Mutanen da ke cikin wannan otel lokacin faruwar lamarin, sun fito ne daga kasashen duniya 14.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.