Isa ga babban shafi
Mali

Harin Mali: An kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su

Wasu majiyoyin tsaro a Mali sun ce babu sauran mutanen da ‘Yan bindiga suka yi garkuwa da su a cikin wata babbar Otel a birnin Bamako, inda akalla mutane 22 suka mutu a yau Juma’a.

An kubutar da dukkanin mutanen da 'Yan Bindiga suka yi garkuwa da su a harin da suka kai ginin Otel din Radisson Blu a Bamako
An kubutar da dukkanin mutanen da 'Yan Bindiga suka yi garkuwa da su a harin da suka kai ginin Otel din Radisson Blu a Bamako AFP
Talla

An shafe sa’o’I da dama ‘Yan bindiga na garkuwa da mutane kusan 170 a cikin ginin Otel na Radisson Blu a Bamako. Rahotanni na cewa mutanen an kubutar da su ne ko kuma sun tsere bayan 30 sun tsere tun da farko.

Kimanin mutane 22 ‘Yan bindigar suka kashe a harin da suka kaddamar da safiyar yau Juma’a.

Mayakan al Qaeda reshen Maghreb sun yi ikirarin daukar alhakin kai harin a ginin Otel din inda baki ‘Yan kasashen waje ke sauka.

Zuwa yanzu babu wani labari game da kame ‘Yan bindigar da suka kai harin na Mali

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.