Isa ga babban shafi
Mali

An cakfe 'yan ta'adda da dama a Mali

Jami’an tsaro a Mali sun sanar da cafke mutane 12 da aka zargi da hannu wajen aikata ta’addanci a kasar, inda yanzu haka ake tsare da su a birnin Bamako.

Sojojin gwamnatin Mali a garin ( à Goundam, kusa da Tombouctou).
Sojojin gwamnatin Mali a garin ( à Goundam, kusa da Tombouctou). AFP/PHILIPPE DESMAZES
Talla

Daga cikin mutanen da aka kama har da wadanda ake zargi da hannu wajen dasa nakiyar ta yi sanadiyyar mutuwar sojojin kasar da dama a yankin Tenenkou, kuma dukkaninsu magoya bayan wata kungiya ce mai suna Macina.

A cikin makonnin da suka gabata jami’an tsaron sun tsananta kai farmaki a yankin tsakiyar kasar ta Mali domin karya lagon wannan sabuwar kungiya da ta bulla a daidai lokacin da dakarun kasar da na kasashen duniya ke ci gaba da fada da wasu kungiyoyin ‘yan bindiga a arewacin kasar ta Mali.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.