Isa ga babban shafi
Afrika ta tsakiya

27 ga Disemba za a yi zabe a Afrika ta tsakiya

Hukumar Zabe a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya mai fama da tashin hankali ta sanar da cewar za a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu a ranar 27 ga watan Disamba mai zuwa.

Bangui babban birnin Jamhuriyar Afrika ta tsakiya
Bangui babban birnin Jamhuriyar Afrika ta tsakiya Wikipedia
Talla

Kafin gudanar da zaben, al’ummar kasar za su gudanar da zaben raba gardama domin amincewa da sabon kundin tsarin mulkin kasar wanda ya amince da wa’adi biyu ga kowanne shugaban kasa na shekaru 5.

Kasashen duniya na ci gaba da matsin lamba ga hukumomin kasar wajen ganin an gudanar da zaben kafin karshen 2015.

Afrika ta tsakiya ta fada cikin rikici ne a 2013 bayan ‘Yan tawayen Seleka yawancinsu Musulmi sun hambarar da gwamnatin Francois Bozize., daga lokacin ne kuma rikicin kasar ya rikide ya koma na addini tsakanin Seleka da anti-balaka Kiristoci.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.