Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

An kona gidaje sama da 100 a Afrika ta tsakiya

Rahotanni daga Janhuriyar Afirka ta Tsakiya sun ce akalla gidaje sama da 100 aka kona, kuma aka yanka wasu a sabon fadan da ya barke a karshen makon da ya gabata.

Afrika ta tsakiya ta fada cikin rikici ne a 2013
Afrika ta tsakiya ta fada cikin rikici ne a 2013 AFP Photo/Edouard Dropsy
Talla

Wata majiyar soji ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar, gawarwakin da suka samu na dauke da harbin bindiga da wasu da aka yanka makogwaransu da wuka.

Yanzu haka daruruwan mazauna Bangui sun gudu sun bar gidajen su.

Wannan na zuwa ne a yayin da Shugaban Darikar Katolika Fafaroma Francis ke shirin kai ziyara a kasar mai fama da rikicin Addini.

Afrika ta tsakiya ta fada cikin rikici ne a 2013 bayan ‘Yan tawayen Seleka yawancinsu Musulmi sun hambarar da gwamnatin Francois Bozize. Daga lokacin ne kuma rikicin kasar ya rikide ya koma na addini tsakanin Seleka da anti-balaka Kiristoci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.