Sama da mutane dubu 2 ke gudun hijira daga Afrika ta Tsakiya
A wani Rahota da ta fitar Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da 'yan gudun hijira 2000 suka tserewa rikicin Afrika ta Tsakiya zuwa Jamhuriyar Demokradiyar Congo a makon da ya gabata.
Wallafawa ranar:
Shugaban hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Antonio Guiterres ya bayana cewa mutanen sun isa yankunan arewa maso gabacin Jamhuriyar Demokradiyar Congo a cikin hali na tagayara.
Shugaban ya kuma soki hukumomin Jamhuriyar Demokradiyar Congo kan yadda suka umurci jami’an tsaro da su rufe kan iyakar kasar da Afrika ta tsakiya.
Tun lokacin da rikici Afrika ta Tsakiya ya barke kasashen dake makwabtaka da su, suka fara rufe iyakokinsu domin kaucewa kutse 'yan gudun hijira.
Shugaban Rikwan kwaryar kasar Catherina Samba Panza da a yanzu ta Umarce zaman makoki a kasar na kwananki uku sakamakon mutuwar mutane da dama a rikici, na ci gaba da kokarin shawo kan rikicin kasar domin samar zaman lafiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu