Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

Shugabar Afrika ta tsakiya ta bukaci Jama'a su koma gidajesu

Shugabar Kasar Janhuriyar Afirka ta Tsakiya Catherine Samba Panza ta bukaci al’ummar kasar da su kwantar da hankulansu, su kuma koma gidajensu bayan tashin hankalin da aka samu a Kasar.

Shugabar Jamhuriyar Afrika ta tsakiya Catherine Samba Panza.
Shugabar Jamhuriyar Afrika ta tsakiya Catherine Samba Panza. RFI/Pierre Pinto
Talla

Rikicin wanda aka kwashe kwanaki uku a na yi, ya yi sanadiyar mutuwar mutane 37 tare da tilasta wa mutane sama da dubu 30 fice wa daga babban birnin Bangui.

Rahotanni sun ce ko a jiya sai da aka ji karar harbe harbe a kusa da tashar jiragen saman kasar inda ake samun tashin hankalin, yayin da akalla mutane dubu 20 suka samu mafaka kusa da sansanin sojojin Faransa da na Majalisar Dinkin Duniya.

Tuni shugaba Panza ta koma gida daga taron Majalisar Dinkin Duniya dan fusknatar matsalar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.