Isa ga babban shafi
ICC

ICC na zargin Ongwen da aikata laifuka 60

Kotun hukunta manyan laifufuka ta duniya ta fitar da jerin zarge-zarge har guda 60 akan mataimakin shugaban kungiyar ‘yan tawayen Uganda LRA Dominique Ongwen, wanda ke tsare a hannun kotun da ke birnin Hague. 

Mataimakin Shugaban Kungiyar 'Yan Tawyen Uganda LRA, Dominic Ongwen
Mataimakin Shugaban Kungiyar 'Yan Tawyen Uganda LRA, Dominic Ongwen AFP PHOTO / INTERPOL
Talla

Dominique Ongwen mai shekaru 40 a duniya ya mika kansa ne ga sojojin Amurka cikin watan janairun da ya gabata a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, kuma shi ne babban jami’in kungiyar LRA na farko da aka cafke tun bayan fitar da sammacin kama shugabannin kungiyar da ke gudanar da ayyukanta a kasashen da dama na tsakiya da gabashin Afirka.

Wasu daga cikin zarge-zargen da ake yi Dominique da kuma sauran shugabannin kungiyar har da Joseph Kony, sun hada da hare-haren da mayakan kungiyar suka rika kai wa tare da kashe fararen hula tsakanin 2003 zuwa 2004 a jamhuriyar Afirka ta tsakiya.

Har ila yau ana zargin Dominique Ongwen da kuma sauran shugabannin kungiyar da kashewa ko kuma azabtar da jama’a tare da sanya yara kanana aikin soji a kasashen Uganda, Sudan ta Kudu da kuma jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo.

Ita dai kungiyar LRA an kafa ta ne tun shekarar 1980 karkashin jagorancin Joseph Kony, kuma daga lokacin zuwa yau dakarun kungiyar sun kashe dubban mutane, yi wa mata fyade, kona garuruwa da dai sauransu, to sai dai duk da cewa an jima da kotun duniya ta fitar sammacin kama Mista Kony amma har yanzu yana ci gaba da boyewa a wani wuri da ke tsakanin Uganda da Jamhuriyar Afirka ta tsakiya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.