Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

Shugabar Afrika ta Tsakiya ta roki Zaman lafiya a Kasar

Shugabar rikwan kwaryar Jamhuriyar Afrika ta tsakiya ta roki zaman lafiya a rikicin kasar da a yanzu Majalisar dinkin duniya ke cewa mutane 36 sun mutu yayin da wasu kusan dubu 30 suka tserewa gidajensu a birnin kasar na Bangui cikin kwanaki Uku. Batun da ke zuwa a dai-dai lokacin da wasu kasashen da ke makwabtaka da kasar ke rufe iyakokinsu domin hana kuste ‘yan gudun hijira. 

Shugabar Rikwan Kwarya a Afrika ta Tsakiya Catherine Samba-Panza
Shugabar Rikwan Kwarya a Afrika ta Tsakiya Catherine Samba-Panza AFP PHOTO / TIMOTHY A. CLARY
Talla

Shugabar rikwan kwaryar Catherina Samba Panza wacce a yanzu ta katse ziyara da ta ke yi a Amurka sakamakon rikcin kasar ta roki al’ummar kasar su bar kura ta lafa.

Yayin da Hukumar ‘yan gudun hijira ta MDD ta c igaba da bayana furgabanta da rikicin da ke neman juyewa irin ta shekarar 2013 zuwa 2014, wadda dubun-dubatan al’ummar kasar suka rasa rayukansu wasun su kuma suka tserewa Muhallinsu.

Mai Magana a madadin hukumar Leo Dobbs wanda ke shaidawa manema labarai mutuwar mutane 36 a da kuma tserewa wasu 27,400 daga gidajensu ya kuma kara da cewa rabin wadanda suka tsere na mafaka ne a fillin tashin jiragen sama na kasa da kasa dake birnin Bangui.

Abin da yanzu haka ya haifar da cunkuso a fillin tashin jiragen.

Rahotanni dai sun ce a sanya shige a kowani kusurwa na kasar, yayin da suma wasu kasashen da ke makwabtaka da Afrika ta tsakiya suka rufe iyakokinsu domin hana kutsen 'yan gudun hijira a cikin kasarsu.

Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya ta fada a cikin wani hali tun lokacin da aka hambarar da tsohon shugaban kasar Francois Bozize a shekarar 2013.

Shugaba Samba Panza ta a ce za a dage zaben kasar da ake shirin gudanarwa a watan Oktoba saboda matsalolin tsaro.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.