Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotu ta soke zaben Darius na Jihar Taraba

Kotun sauraren kararrakin Zabe a Taraba arewacin Najeriya ta soke zaben gwamnan Jihar Darius Ishaku na Jam’iyyar PDP a yau Assabar tare da tabbatar da Hajiya Aisha Jummai Alhassan a matsayin wadda ta lashe zaben na gwamna.

Sanata Aisha Jummai Alhassan ta Jam'iyyar APC ta yi watsi da zaben Gwamnan Taraba a Najeriya
Sanata Aisha Jummai Alhassan ta Jam'iyyar APC ta yi watsi da zaben Gwamnan Taraba a Najeriya REUTERS
Talla

Alkali mai shari’a Musa Danladi Abubakar ya bayar da umurnin gaggauta rantsar da Hajiya Aisha Jummai Alhassan a matsayin gwamnan Jihar wacce ta kalubalanci zaben Darius na Jam’iyyar PDP.

Kotun ta soke zaben ne akan dalilin Jam’iyyar PDP ba ta yi cikakken zaben fitar gwani ba, baya ga kuma korafe korafen da Jummai Alhassan ‘Yar takarar APC ta shigar na zargin an tabka magudi a zaben gwamnan da aka gudanar a watan Afrilu.

A tarihin siyasar Najeriya dai wannan ne karon farko da aka zabi Mace a matsayin gwamna bayan Kotun sauraren kararrakin zaben na Taraba ta tabbatar da Hajiya Aisha Alhassan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.