Isa ga babban shafi
Najeriya

Aisha Alhassan za ta garzaya Kotu

Sanata Aisha Jummai Alhassan da ta nemi zama Mace ta farko a matsayin Gwamna a tarihin siyasar Najeriya ta ce za ta garzaya Kotu domin kalubalantar sakamakon zaben jihar Taraba bayan hukumar zabe ta bayyana Darius Dickson Ishaku na Jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben.

Sanata Aisha Jummai Alhassan ta Jam'iyyar APC ta yi watsi da zaben Gwamnan Taraba a Najeriya
Sanata Aisha Jummai Alhassan ta Jam'iyyar APC ta yi watsi da zaben Gwamnan Taraba a Najeriya REUTERS
Talla

Hukumar zaben Jihar ta ce Dan takarar Jam’iyyar PDP ya lashe zaben ne da yawan kuri’u 369,318, yayin da Aisha Alhassan ta APC ta zo a matsayi na biyu da yawan kuri’u 275,984 bayan sake zaben a ranar Assabar.

A ranar 11 ga watan Afrilu ne aka gudanar da zaben gwamnoni a jihohin Najeriya amma saboda wasu matsaloli da aka samu a Jihohin Imo da Taraba da Abia ya sa hukumar INEC ta ce a sake zaben

Jam’iyyar APC  ta yi watsi da sakamakon zaben ne saboda zargin an yi magudi.

Sakamakon zaben dai na nuna Jam’iyyar PDP da ta sha kaye a zaben shugaban kasa ta samu karin kujerar gwamna guda bayan ta lashe Jihar Gombe kacal a arewacin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.