Isa ga babban shafi
Najeriya

Zaben Najeriya: An girke ‘Yan sanda a Jihar Rivers

Rundunar ‘Yan sandan Najeriya tace ta karfafa tsaro a wasu jihohin kasar da ake fargabar samun rikici a zaben gwamnoni da ake gudanarwa a yau Assabar. A Jihar Rivers da ke kudancin kasar an linka ‘Yan sanda fiye da wadanda aka tura a zaben shugaban kasa.

sufuto Janar na 'Yan sandan Najeriya Suleiman Abba
sufuto Janar na 'Yan sandan Najeriya Suleiman Abba facebook
Talla

Babban sufeton ‘Yan sandan Najeriya Suleiman Abba ya shaidawa Rediyo Faransa cewa sun kara yawan Jami’an tsaro a Jihohin Rivers da Gombe da Filato da Lagos da Imo da Akwa Ibom da Benue.

Kuma an aika da karin kwamishinonin ‘Yan sanda guda biyu a Jihohin domin kula da sha’anin tsaro a lokacin zabe.

05:23

Sufuto Janar na 'Yan Sanda Suleiman Abba

Bashir Ibrahim Idris

Mr Abba ya ce sun aika da ‘Yan sanda fiye da 2000 a Jihar Rivers inda ‘Yan adawa ke zargin an yi magudi a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 28 ga watan Maris.

‘Yan adawa dai na zargin ana hada baki ne da Jami’an tsaro wajen yin magudi tare da hana su shedawa.

Amma sufeto na ‘Yan sandan na Najeriya ya tabbatar da cewa za a yi zaben cikin nasara fiye da zaben shugaban kasa da aka gudanar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.