Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan bindiga sun kashe mutane da dama a jihar Rivers dake Najeriya

Yayin da ake shirin yin zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar Jihohi cikin karshen mako a Nigeria, wasu ‘yan bindiga sun afka wasu kauyukan jihar River dake yanki Neja Delta a Nigeria, inda suka kashe a kalla mutane 9, tare da raunata wasu 2. Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar ta River Ahmad Muhammad, yace a daren ranar juma’a ‘yan bindiga daba a san ko su waye ba, suka far wa kauyukan Obrikom da Obor, inda suka kashe mutane tare da kone gidaje.Mai magana da yawun ‘yan sndan yace ‘yan bindigan sun kuma kone gidan wani dan siyasa mai suna Vincent Ogbagu, dake takarar majalisar dokokin jihar ta River.Dama Jihar ta River na daya daga cikin jihohin da aka sami tashe tashen hankula, a lokacin zaben shugabancin kasa, da aka yi a karshen makon daya gabata. 

Wasu masu gwagwarmaya da makamai a yankin Niger Delta na Najeriay
Wasu masu gwagwarmaya da makamai a yankin Niger Delta na Najeriay AFP/PIUS UTOMI EKPEI
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.