Isa ga babban shafi
Najeriya

Ana zaben Gwamnoni a Najeriya

Al’ummar Najeriya na gudanar da zaben gwamnoni da ‘Yan Majalisun Jiha a yau Assabar bayan sun gudanar da zaben shugaban kasa da ‘Yan Majalisun Tarayya makwanni biyu da suka gabata inda Jam’iyyar adawa ta lashe zaben.

An tatance Shugaban Tarayyar Najeriya Gooluck Ebele Jonathan a zaben gwamnoni a mazabarsa da ke Jihar Bayelsa
An tatance Shugaban Tarayyar Najeriya Gooluck Ebele Jonathan a zaben gwamnoni a mazabarsa da ke Jihar Bayelsa twitter
Talla

Daga cikin Jahohi 36 na Najeriya, za a gudanar da zaben gwamnoni ne a Jihohi 29 yayin da a jihohi 36 na kasar kuma za a gudanar da zaben ‘Yan majalisar Jiha.

Wakilinmu na Jihar Bauchi Shehu Saulawa ya ce tuni aka fara tattance masu kada kuri’a a wasu runfunan zabe a Jihar Gombe.

A garin Owerri na Jihar Imo a kudancin kasar, Faruk Muhammad Yabo ya ce Jami’an zabe sun fito da wuri.

A Jihar Sokoto, wakilinmu Abdulkarim Ibrahim Shikal ya ce Jami’an zabe sun yi sammako amma mutane sun yi jinkirin fitowa runfunan zabe.

Jam’iyyar PDP da ta sha kaye a zaben shugaban kasa tana da gwamnoni 21 a jihohin kasar yanzu haka, yayin da Jam’iyyar APC ke da yawan gwamnoni 14.

Sai dai kuma a zaben na yau ana ganin APC za ta yi mamayar Jihohi da dama bayan dan takararta Janar Muhammdu Buhari ya lashe zaben.

Hukumar zaben Najeriya ta ce ta dauki darussa da dama a zaben shugaban kasa da aka gudanar tare da bayyana fatar samun nasara musamman saboda fuskanci matsaloli daga na’urar tantance masu jefa kuri’a da kuma tsaikun zuwan malaman zabe.

A ranar zaben hukumar ‘Yan sandan Najeriya ta takaita zirga-zirgar ababen hawa har sai an kammala jefa kuri’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.