Isa ga babban shafi
Najeriya

Majalisar jihar Taraba ta kafa kwamitin tantance lafiyar Suntai

Shugaban Majalisar Dokokin jihar Taraba a tarayyar Najeriya Joshia Kente ya nada kwamitin mutane 5 dan tantance lafiyar gwamnan jihar Danfulani Danbaba Suntai da ke shirin karbar ragamar tafiyar da jihar bayan ya dawo daga birnin London inda ya yi jinya.  

Gwamnan jihar Taraba Danbaba Suntai
Gwamnan jihar Taraba Danbaba Suntai
Talla

Wata sanarwa da shugaban majalisar jihar Mista Kente ya raba wa manema labarai a garin Jalingo, ta ce matakin ya biyo bayan bukatar hakan ne da ta fito daga zaman majalisar kwamishinonin jihar da aka gudanar a ranar 10 ga wannan wata na satumba, wanda ya bukaci a kafa wannan kwamiti.

Sanarwar ta bayyana Farfesa Bala Sheku a matsayin shugaban kwamitin, sai likitan gwamnan Danbaba Dr Ahmed Kara, da Farfesa Peter Alabi, da Dr Shehu Sule da kuma wani mai suna Dr Inuwa Sama’ila.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.