Isa ga babban shafi
Najeriya

Dawowar Suntai ya haifar rikicin Siyasa a Taraba

Dawowar Gwamna Dan Baba Suntai da wasu suka kira mai rashin lafiyar Nakasa, bayan Jinyar da ya dade yana fama da ita a Assibiti dake a kasashen waje, ta haifar da rudani a jihar Taraba.

Gwamna Dan Baba Suntai na Taraba Najeriya
Gwamna Dan Baba Suntai na Taraba Najeriya pmnewsnigeria.com
Talla

Rahotanni daga jihar dai na bayyana cewar Majalisar Dokokin jihar dai ta bukaci Gwamnan da ya bayyana a gabanta domin kare Takardar bukatar komawa a kan Kujerar gwamnan, da aka gabatar mata da cewar Gwamna Dan Baba Suntai ne ya rubuta ta.

Sai dai da dama daga cikin al’ummar Jihar na zargin cewar wasu na kusa da gwamnan ne suka kirkiri Takardar ba Gwamnan ba, kamar yanda aka bayyana cikin Takardar da aka gabatarwa Majailisar.

A karshen Satin daya gabata ne dai aka ga gwamna Suntai dake dawowa daga jinya, na sauka daga Jirgi tare da taimakon wasu makusantan sa, a yayinda aka hana mukaddashin gwamna, kuma mataimakin sa isa kusa da shi, abinda ya haifar da Ayar tambaya ga sahihancin lafiyar sa.

Yanzu haka dai wasu da suka kira kansu kungiyar dake neman ganin anyi adalci a Jihar Taraba, a karkashin jagorancin John Ambulus, sun bukaci tsige gwamnan Jihar Taraba, da kuma hukunta duk wadanda keda hannu wajen dauko shi daga inda yake jinya dan dawo da shi gida su biya bukatun kansu.

Yayin da yake ganawa da manema labarai a Abuka, John Ambulus yace, ta bayana cewar rashin lafiyar Gwamna Danbaba Suntai a bayyan yake, saboda haka ba zai iya gudanar da mulki ba, inda suka bukaci shugaban kasa da ya gagauta daukar mataki akai.

A bangare daya kuma fitaccen lauyan Nigeria, Femi Falana ya bukaci Sufeto Janar an Yan Sandan kasar da ya binciko wadanda suka sanya hannu a wasikar da akace Danbaba Suntai ya sanya hannu wanda aka mikawa Majalisa cewar ya dawo zai cigaba da aiki.

Falana yace nemo wadanda sukayi sojan-Gona wajen sanya hannu a wasikar da kuma hukunta su ya zama wajibi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.