Isa ga babban shafi
Najeriya

Babu shakku akan Mutuwar Shekau, inji Gwamnatin Najeriya

Hukumomi a Tarayyar Najeriya sun ce a game da irin bayanan da suke ci gaba da tattarawa, ko shakka babu an kashe shugaban kungiyar Boko Haram Malam Abubakar Shekau, inda a makon jiya rundunar Sojin kasar suka ce wata kila Shekau ya mutu bayan sun harbe shi a wata Musayar wuta.

Shugaban Kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau da aka yi ikirarin kila ya mutu a Najeriya
Shugaban Kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau da aka yi ikirarin kila ya mutu a Najeriya
Talla

Ministan harkokin cikin gidan kasar Patrick Abba Moro, ya shaidawa gidan Rediyo Faransa cewa, jagoran na Boko Haram ya mutu ne sakamakon raunukan da ya samu a lokacin artabun da aka yi tsakaninsu da sojojin kasar a kwanakin da suka gabata.

“Bai kamata a ci gaba da nuna shakku dangane da wannan batu ba” inji Ministan.

Sojin na Najeriya sun ce Shekau ya mutu ne a tsakanin 30 ga watan Yuni amma akwai sabanin kalamai da ke karo da juna daga ikirarin na sojin akan mutuwar shekau.

Abba Moro yace sun yi imani da abinda Sojin na Najeriya suka ce game da Mutuwar Shekau.

“Dukkanin bayanan da aka tattara sun tabbatar da Shekau ya mutu”, a cewar Ministan.

A cikin sanarwar Sojin na Najeriya sun ce suna tunanin Shekau ya mutu ne tsakanin ranar 25 ga watan Yuli zuwa ranar 3 ga watan Agusta.

Sanarwar tace Shekau wanda Najeriya da Amurka ke nema ruwa a jallo a matsayin Dan ta’adda, Sojojin sun harbe shi ne a ranar 30 ga watan Yuni a wata musayar wuta da suka yi a sansanin Kungiyar da ke Sambisa.

Sojojin sun ce an kwashi Shekau zuwa wani wuri da ke kan iyaka da kasar Kamaru domin jinya bayan sun harbe shi. amma Akwai kalamai masu karo da juna a cikin sanarwar Sojin na Najeriya, domin da farko sun ce kila ya mutu amma kuma a wani wurin sai suce tabbas ya mutu.

Tuni, dakarun na Najeriya suka yi ikirarin samun nasara akan kungiyar Boko Haram amma akwai jerin hare hare da ake ci gaba da kai wa musamman a yankunan arewa maso gabaci da aka kafawa dokar ta-baci.

Akwai kwamitin da Gwamnatin Jonathan ta kafa domin sasantawa da Boko Haram, kuma kwamitin ya yi ikirarin zantawa da shugabannin kungiyar amma Abubakar Shekau ya fito a wani hoton Bidiyo yana karyata ikirarin.

Har Yanzu ‘Yan Najeriya suna jiran martanin Kungiyar Boko Haram domin tabbatar da mutuwar Shugabansu.

Kodayake akwai wata Kafar Yada Labarai ta kasar waje da ta Ruwaito wani Mamban Boko Haram yana tabbatar da cewa lalle Shekau ya Mutu.

Amma Masana suna ganin kashe Shekau ba shi zai kawo karshen Matsalar tsaro ba a Najeriya domin akwai wasu ‘Yan bindiga da dama da ke fake wa da sunan kungiyar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.