Isa ga babban shafi
Nigeria

An Kashe Mutane 10 A Rikicin Jihar Taraba Nigeria

Akalla mutane goma suka ransa rayukansu yayin da wasu da dama suka samu raunuka, bayan da wasu matasa ‘yan kabilar Jukun suka kai hari a garin Jibo dake karamar hukumar Wukari.Kakakin Rundunar ‘Yan sandan Jihar, Joseph Kwaji, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce baya ga rayuka da aka rasa an kona gidaje da dukiyoyi da dama, inda ya kara da cewa amma yanzu haka kura ta lafa.Jihar Taraba na daga cikin jihohin da ake fama da tashe-tashen hankula da kashe-kashe a Nigeria.Yanzu haka garin Ibbi na cikin dokar hana fita kwata-kwata sakamakon fadar da ake ganin na kabilanci ne da ya kaiga rasa rayukan jama'a. 

Danbaba Suntai gwamnan Jahar Taraba da ke jinya a gida
Danbaba Suntai gwamnan Jahar Taraba da ke jinya a gida RFI Hausa
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.