Isa ga babban shafi
Chadi

Mutanen da suka mutu a zamanin Habre sun zarce 40,000 a Chadi

Shugaban Hukumar binciken tsohon shugaban kasar Chadi Hissene Habre ya ce adadin mutanen aka kashe a zamaninsa ya zarce adadin mutane 40,000 da aka gabatarwa Kotun da farko, domin kididdigar da suka yi ya nuna cewar an halalka mutane fiye da haka.

Tsohon Shugaban Chadi Hissène Habre da ke fuskantar Shari'a a Chadi
Tsohon Shugaban Chadi Hissène Habre da ke fuskantar Shari'a a Chadi AFP PHOTO / SEYLLOU
Talla

Tsohon shugaban na Chadi na fuskantar shari’a ne a Kotun kasar Senegal kan aikata laifukan yaki.

A Yayin da ya ke bayar da bahasi a gaban kotun da ke shari’ar tsohon shugaban na Chadi a Dakar, shugaban da ke binciken Mahamat Hassan Akbar ya ce a cikin kwanaki kusan 3 da Habre ya yi yana mulkin kasar, a kowace rana an kashe adadin mutane 13.

Akbar ya fadi haka ne bayan ya gabatar da shaidun da suka tattara daga wadanda suka bada shaida akan ta’asar tsohon shugaban na Chadi.

Akbar ya ce kashi 98 na shaidun da suka tattara sun same su ne a birnin Ndjamena da kewaye kan tsohon shugaban wanda a baya ake kiran sa Pinochet na Afirka, Wato tamkar tsoshon shugaban kama karya na Chile.

Kimanin adadin mutane 40,000 aka ce sun mutu a zamanin mulkin shi a Chadi. Amma Akbar da ke jagorancin hukumar binciken ya ce wannan kiyasin na kashi 10 ne akwai daga cikin adadin mutanen da suka mutu a zamanin mulkin tsohon shugaban na Chadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.