Isa ga babban shafi
Senegal-Chadi

Da karfi aka shigar da Habre a Kotun Senegal

Jami’an tsaro sun sake yin amfani da karfin domin gabatar da tsohon shugaban kasar Chadi Hissene Habre a gaban kotun musamman ta Afirka da ke kasar Senegal a yau Litinin, inda ake tuhumar sa da aikata laifufuka lokacin da ya ke mulkin kasar Chadi daga shekarar 1982 zuwa 1990.

An sake shigar Tsohon Shugaban Chadi Hissène Habré da karfi a Kotun Senegal
An sake shigar Tsohon Shugaban Chadi Hissène Habré da karfi a Kotun Senegal AFP PHOTO / SEYLLOU
Talla

Kotun da ke birnin Dakar ta koma zamanta ne bayan da aka bai wa bangaren masu shigar da kara da wadanda ake tuhuma tsawon kwanaki 45 domin kara kintsa wa shari’ar.

Sai dai kamar yadda aka gani a zaman kotun na farko, Tsohon shugaban kasar ta Chadi Hissene Habre, ya ki bayyana a gaban masugudanar da shari’ar lamarin da ya sa aka share tsawon sa’o’i biyu ana jiransa amma ba tare da ya bayyana ba, kafin alkalai su bai wa jami’an tsaro umurnin yin amfani da karfin tuwo domin gabatar da shi.

Tsohon shugaban na Chadi ya fito ne a cikin fararen kaya sanye da rawani, inda ya rika furta kalamai na rashin amincewa da kafuwar kotun, wadda ya bayyana a matsayin mai karba umurnin ‘yan mulkin mallaka.

Bayan ya kammala furta kalamansa na ashar a cikin zauren kotun ne, sai alkalin da ke jagorantar shari’ar Gberdao Gustave Kam dan kasar Burkina Faso, ya bayar da umurnin karantawa Habre zarge-zargen da ake yi ma sa.

Magoya bayansa dai sun rika yin ihu a cikin kotun kafin fitar da su daga zauren.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.