Isa ga babban shafi
Chadi

Macky Sall zai gurfanar da tsohon shugaban kasar Chadi Habre a gaban kotu

Shugaban kasar Senegal, Macky Sall, ya ce nan ba da dadewa ba za’a gurfanar da Tsohon shugaban kasar Chadi, Hissen Habre, a gaban kotu, maimakon mika shi ga wata kasa.

Shugaban kasar Senegal, Macky Sall.
Shugaban kasar Senegal, Macky Sall. DR
Talla

Shugaba Sall ya bayyana haka ne a taron shugabanin kasashen Afrika a Addis Ababa, inda yake cewa, matsin lambar daga kasahsen duniya, ya sa za’a gurfanar da tsohon shugaban a kotun Dakar.

A kwana nan, Sakatariyar harkokin kasar wajen Amurka, Hillary Clinton, ta yi kira ga kasashen yammacin Afrika da su tabbata an binciki tsohon shugaban kasar Habre.
 

Ana zargin Habre, dan shekaru 70, da aikata manyan laifuka da su ka hada da kisa a mulkin shi da ya kwashe shekaru takwas ya na yi a kasar ta Chadi.

Shekaru 20 da su ka gabata, Habre ya tsalleke zuwa kasar Senegal a domin neman mafaka bayan an hambare gwamnatinsa a juyin mulkin da aka gudanar a shekarar 1990.

Kasar Belgium wacce bagaren shari’ar ta ya yadda da ta gurfanar da wanda a ke zargi da manyan laifuka ta dade tana neman Majalisar Dinkin Duniya da ta tilasta kasar Senegal ta gurfanar da Habre a gaban kotu ko kuma ta mika shi ga inda ya dace a bincike shi.

Sai dai a cewar Ministan Shari’a a kasar ta Senegal, Aminata Toure, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran AFP ya fada, ya fi dacewa Habre ya fuskanci hukuma dai dai da tsarin da Kungiyar Tarayyar Afrika ta tanada.

Ta kara da cewa kasar ta Senegal ta na da tabbacin cewa, kasashen Afrika musamman kasar Senegal na da tsarin da zai iya hukunta tsohon shugaban kasar na Chadi.

Ganin cewar Kotun Manyan Laifuka ta duniya ta fi mai da hankali a kan shugabannin nahiyar ta Afrika, ya sa wasu da dama na ganin cewa gara nahiyar ta Afrika ta dinga daukan nauyin hukunta wadanda ake zargi da laifuka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.