Isa ga babban shafi
Nijar

Boko Haram ta kashe mutane uku a Abadam kudancin Nijar

Wasu da ake hasashen Mayakan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari a kusa da garin Abadan da ke kan iyakar kasar Jamhuriyyar Nijar da Najeriya inda suka kashe mutane uku cikinsu har da sojan kasar daya.

Yankin Diffa na cikin dokar ta-baci a Jamhuriyyar Nijar
Yankin Diffa na cikin dokar ta-baci a Jamhuriyyar Nijar AFP PHOTO / PIUS UTOMI EKPEI
Talla

Kamfanin dillancin labarai Reuters ya ruwaito wata wata majiyar sojan Nijar ta tabbatar da cewa an hallaka ilahirin ‘yan ta’addar da suka kai harin a yankin Jihar Diffa kudancin Nijar.

Yankin Diffa dai na fama da matsalar ‘Yan Boko Haram. Kuma kimanin ‘Yan gudun hijira 150,000 suka tsallaka yankin daga Najeriya saboda rikicin Boko Haram.

Yanzu haka dai yankin Diffa na cikin dokar ta-baci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.