Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta damu da rikicin Boko Haram

Shugaban Faransa Francois Hollande, ya bayanna damuwar akan rikicin Boko Haram, a lokacin ya ke ganawa da jakadojin kasashen duniya a birnin Paris.

Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya ce yana nan a raye a cikin wani sakon sauti
Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya ce yana nan a raye a cikin wani sakon sauti AFP/Capture d'écran vidéo
Talla

Shugaban ya ce Faransa za ta shirya wani taron da zai hada shugabannin kasashen da ke fama da rikicin Boko Haram da niyya hada kansu don kawo karshen matsalar kungiyar.

A lokacin da ya ke gabatar da jawabi a gaban jekadojin kasashen duniya, Shugaba Hollande ya ce ta’addanci babbar matsala ce da dukiya ke fama da ita a wannan zamani, inda ya bayar da misali da kungiyar ISIL da Boko Haram ke ci gaba da aikata miyagun laifufuka a sassan duniya.

Shugaban ya ce ya zama wajibi a taimaka wa Najeriya domin kawo karshen Kungiyar Boko Haram.

Kungiyar Boko Haram ta kashe mutane sama da dubu goma a bana kawai, yayin da a bara ta kashe fiye da dubu 14, mafi yawansu mata da kananan yara.

Hollande ya ce Kungiyar yanzu ta zama barazana ga kasashe Makwabta, kuma alhaki ya rataya a wuyan Shugabannin duniya don taimaka wa kasashen da rikicin ya shafa.

Shugaban na Faransa ya ce nan da ‘yan kwanaki kadan zai gana da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, domin tattauna batun Boko Haram.

Hollande dai ya taba jagorantar taron Boko Haram da Shugabannin kasashen Najeriya da Chadi da Kamaru da Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.