Isa ga babban shafi
Mali-MDD

An ceto mtutanen da 'yan bindiga suka yi garkuwa dasu a Mali

An ceto ‘yan kasashen waje 5, yayinda aka sako wasu mutanen da ‘yan bindiga suka yi garkuwa dasu, yayin wani gumurzu tsakanin ‘yan bindigan da Sojojin garin Sevare dake tsakiya kasar Mali. Yau Asabar Wata majiyar sojan kasar tace, Lamarin da ya faru a wani Otel mai suna Byblos, ya kuma yi sanadiyyar rasa ran a kalla mutane 7. 

Wasu sojan kasar Mali suna bakin aiki
Wasu sojan kasar Mali suna bakin aiki AFP PHOTO / JOEL SAGET
Talla

Jami’an gwamnati sun ce jiya juma’a, ‘yan bindigan suka afka cikin Otel din da baki ke yawan zuwa, kuma kafin sojan su mayar da martani ‘yan bindiga suka yi garkuwa da mutanen dake wajen.
Wata majiya tace akwai ‘yan kasashen Afrika ta Kudu, Faransawa da dan kasar Ukraine a cikin Otel din lokacin da aka kai harin.
Kokarin dakarun kasar na tunkarar ‘yan bindigan ya sami koma baya, saboda kasancewar wadanda aka yi garkuwa dasu.
Wata sanarwar rundunar samar da zaman lafiyan Majalisar Dinkin Duniya ta MINUSMA a kasar, tace akwai jami’inta daya cikin wadanda suka rasa ransu a cikin gumurzun.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.