Isa ga babban shafi
Mali

Yarjejeniyar zaman lafiyan kasar Mali na tangal tangal

Rahotannin dake fitowa daga kasar Mali sun ce ‘yan tawayen dake goyan bayan gwamnatin kasar sun ki ficewa daga garin Menaka dake Arewacin kasar, matakin da ake ganin karan tsaye ne ga shirin zaman lafiyar kasar.

Garin Menaka dake Arewacin kasar Mali
Garin Menaka dake Arewacin kasar Mali Sonia Rolley / RFI
Talla

Su dai mayakan sun kwace garin ne daga hannun ‘yan tawayen Abzinawa a watan Afrilu bayan fafatwar da suka yi wadda ta karya yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla.

Sai dai mai magana da yawun ‘yan tawayen Haroun Toureh, yace mutanen garin ne suka bukaci su cigaba da zama dan kare lafiyar su.

A baya bayan nan yawancin kungiyoyin dake dauke da makamai a kasar ta Mali sun sa hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta da aka kulla a kasar Aljeriya, sai dai kuma wani harin da aka kai wa jami’an tsaro a farkon wannan watan ya diga ayar tambaya kan dorewar yarjejeniyar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.