Isa ga babban shafi
Mali

An kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin gwamnati da 'yan tawayen Mali

GWAMNATIN Kasar Mali ta sanya hannu akan yarjejeniyar zaman lafiya da wasu kungiyoyin dake dauke da makamai a Arewacin kasar sai dai kungiyar Azbinawa ta bukaci Karin lokacin kafin amincewa da yarjejeniyar.Yarjejeniyar ta biyo bayan watanni 8 da aka kwashe ana mahawara da kuma lallashin juna tsakanin bangarorin dake dauke da makamai a kasar da kuma bangaren gwamnati da taimakon kasar Algeria.Sai dai kungiyar Abzinawan kasar ta bukaci bata karin lokaci domin ganawa da shugabanin ta kafin sanya hannu kan yarjejeniyar.Kungiyar tace duk wata yarjejeniyar sai ta samu amincewar yayanta kafin tayi tasiri.Sai dai kakakin kungiyar Mohammed Ousmane Mohammedoun, ya bayyana fatar sa na ganin suma sun sanya hannu kan yarjejeniyar da zata kaiga baiwa arewacin Mali kwarya kwaryar yanci nan bada dadewa ba.Shi kuwa ministan harkokin wajen Mali Abdoulaye Diop ya bayyana cigaban da aka samu a matsayin matakin farko na samun zaman lafiya, yayin da ita ma kasar Faransa ta bayyana farin cikin ta da matakin. 

Fraiministan kasar Mali Modibo Keita
Fraiministan kasar Mali Modibo Keita AFP PHOTO / HABIBOU KOUYATE
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.