Isa ga babban shafi
Mali-Faransa

An hallaka Turawa da dama a wani harin ta'addancin da aka kai a Mali

An bindige wasu mutane 5, da suka hada da ‘yan kasashen Faransa da Belgium, yayin wani harin da aka kai cikin daren jiya juma’a, a wani wajen cin abinci dake Bamako, babban birnin kasar Mali. Wani dan sanda da wakilin kamfanin dillancin labarum Faransa na AFP da ke wajen, sun tabbatar da harin, da wani dan sanda ya bayyana harin da na ta’addanci.Wani Jam’in ‘yan sandan da ke wajen yace wani dan sanda da harin ya rutsa dashi wucewa ya zo yi.A halin da ake ciki Shugaban Faransa Francois Hollande yayi Allah wadai da harin na birnin Bamako, inda fadar shugaban tace maharan matsorata ne.Sanarwar da fadar shugaban ta fitar yau Asabar, tace nan ba da dadewa ba shugaba Hollande zai gana da takwaranshi na Mali Ibrahim Boubacar Keita.Cikin abubuwan da shugabanni 2 zasu tatauna hard a yadda faransa zata taimaka da yaki da ayyukan ta’addanci a Mali. 

Shugaban kasar Mali, Ibrahim Boubacar Keïta
Shugaban kasar Mali, Ibrahim Boubacar Keïta RFI/Pierre René-Worms
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.