Nkurunziza ya lashe zaben Kasar Burundi
Hukumar Zaben kasar Burundi ta bayyana shugaba mai ci Pierre Nkurunziza a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar daka aka yi ranar Talata da ta gabata.
Wallafawa ranar:
Hukumar zaben ta ce Nkurunziza ya samu fiye da kashi 69 cikin 100 na kuri’un da aka kada, kuma wannan ya bashi nasara a zaben, ba tare da bukatar zuwa zagaye na biyu ba.
Tuni jam’iyyun adawar kasar, dama manyan kasashen duniya, suka sa kafa suka yi fatali da zaben, da suka bayyana da cewa haramtacce ne, da bai da sahihanci.
Burundi ta tsinci kanta a halin rikici tun bayan da Nkurunziza ya bayyana aniyarsa ta neman shugabancin kasar a wa’adi na uku yayin da ‘yan adawa suka bayyana cewa kasar zata shiga mawuyacin hali fiye da wanda take ciki matukar Nkurunziza ya lashe zaben.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu