Isa ga babban shafi
Burundi

An kai hare hare a rumfunan zaben Burundi

Wasu gungun Mahara sun jefa gurneti a wasu runfunan zabe a sassan birnin Bujumbura fadar gwamnatin Burundi, lamarin da ke neman dagula zaben ‘Yan Majalisu da ake gudanarwa a yau Litinin.

An baza Jami'an tsaro a Bujumbura domin zaben 'Yan majalisun Burundi
An baza Jami'an tsaro a Bujumbura domin zaben 'Yan majalisun Burundi AFP PHOTO / MARCO LONGARI
Talla

Wannan matakin na zuwa ne bayan shafe tsawon watanni biyu al’ummar Burundi na zanga-zangar adawa da matakin shugaban Pierre Nkurunziza na neman wa’adin shugabanci na uku.

Rahotanni sun ce har yanzu ba a soma gudanar da zaben ‘Yan Majalisun ba a sassa da dama na Burundi sakamakon hare haren da aka kai a runfunan zabe.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira a dage zaben saboda tashin hankalin da ya yi sanadiyar rasa rayukan mutane da dama, da kuma ‘Yan adawa da suka ce zasu kauracewa zaben.

Zaben ‘Yan Majalisun dai shi ne mataki na farko kafin zaben shugaban kasar da za a yi ranar 15 ga watan gobe.

Hukumar zaben Burundi ta ce ta shirya tsaf don gudanar da zaben duk da rahotanin kona kayan zaben.

Shugaban hukumar zaben Pieere Claver Ndayicariye ya ce tuni aka raba kayan aiki zuwa mazabu 11,000 na fadin kasar.

Yanzu haka Shugaban Majalisar Burundi Pie Mtavyohanyuma ya tsallake ya bar kasar zuwa Brussels saboda abin da ya kira tashin hankalin da ake samu a kasar, inda ya bukaci shugaban Nkurunziza ya kaucewa tsayawa takarar neman wa’adi na uku.

Shugaban majalisar ya shaidawa wata tashar Talabijin din Faransa cewar yanzu haka yana Brussels saboda halin kuncin da kasarsu ta samu kan ta saboda bukatar shugaba Nkurunziza wanda ya takara ya sabawa kundin tsarin mulki.

Kungiyar Kasahsen Afirka ta AU ta ce ba za ta tura jami’anta ba zuwa Burundi domin sanya ido kan zaben ba saboda rashin yanayi mai kyau na gudanar da zaben wanda ya gamu da tashin hankali da kuma rasa rayuka.

Shugabar gudanarwar kungiyar Nkosazana Dlamini Zuma ta ce babu yadda za a yi a gudanar da karbabben zabe mai sahihanci a irin yanayin da Burundi ta samu kanta a ciki.

Dubban ‘yan kasar ne dai suka gudu zuwa kasashe makwabta don kaucewa tashin hankali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.