Isa ga babban shafi
Burundi

Shugaban Majalisar Burundi ya tsallake ya bar kasar.

Shugaban Majalissar kasar Burundi Pie Ntayyohanyuma ya fice daga kasar saboda halin da kasar ke kara fadawa a ciki kwana guda, a gudanar da zaben ‘yan majalisu.

RFI/ Sonia Rolley
Talla

Pie ya ce ya zama dole ya bar kasar, lura da cewar kudirin shugaban kasar Pierre Nkurunziza wanda bai dace ba, na kara jefa kasar acikin mawuyacin hali.

Majalisar dinkin duniya dai na cigaba da gargadi Burundi a kan wannan zabe, duk da dai tuni hukumar zaben kasar ta fara raba kayayyakin zabe, da ake saran al’umma kasar za su fita gobe litinin domin kada kuri’unsu.

Yan adawar kasar sun ce zasu kauracewa zaben yayin da Sakatare janar na Majalisar Ban-Ki Moon ya bada shawara dage zaben zuwa wani lokaci nan gaba.

Dubban yan kasar ne suka gudu zuwa kasashen makwabta dan kaucewa tahsin hankalin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.