Isa ga babban shafi
Mali

Mayakan Jihadi sun kashe Sojin mali

A kasar Mali, sojoji uku ne suka rasa rayukansu a wani hari da mayakan jihadi suka kaddamar a garin Nara dake kudu maso yammacin Kasar kuma ke kan iyaka da Kasar Mauritania.

Sojin Mali a fagen daga
Sojin Mali a fagen daga REUTERS/Joe Penney
Talla

A wata sanarwa da gwamanatin Kasar ta fitar, ta bayyana bakin cikin mutuwar jami’a sojinta kuma ta kara da cewa , dakarunta sun yi nasarar hallaka mutane 9 daga cikin mayakan jihadin bayan sun mayar da martani.

Wata majiyar ta bayyana cewa an samu miyagun kwayoyi a cikin aljihun daya daga cikin mayakan jihadin da aka kashe.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.