Isa ga babban shafi
Faransa-Mali

Faransa ta bayyana goyon bayanta ga shirin zaman lafiyar kasar Mali

Ministan harkokin tsaron kasar Faransa Jean-Yves Le Drian dake ziyarar aiki a kasar Mali ya jaddada goyon bayan kasarsa na ganin an samu dawamammamen zaman lafiya a kasar. Ziyarar dai na a matsayin karfafa goyon bayan Faransa ga yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a ranar asabar da ta gabata ne tsakanin Gwamnatin kasar da Yan tawaye.  

Ministan Tsaron kasar Faransa, Jean-Yves Le Drian tare da shugaban kasar Mali  Ibrahim Boubacar Keïta a Bamako, ranar 22 Yuni 2015.
Ministan Tsaron kasar Faransa, Jean-Yves Le Drian tare da shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keïta a Bamako, ranar 22 Yuni 2015. AFP PHOTO / HABIBOU KOUYATE
Talla

Bayan ganawa da shugaban kasar Mali Ibrahim Boubakar Kaita Jean Le Drain ya kai ziyara a sansanin sojin kasar Faransa dake garin Gao, a jawabin da ya gabatar ga sojojin, ya ce Faransa zata cigaba da aiki da Gwamnatin Mali wajen ganin an sami Dawamammen zaman lafiya a daukacin fadin kasar ta Mali.

Sai dai ya yi gargadin cewa, akwai wasu kalubale da dama a gabansu, inda ya nemi sojojin dasu kara zage dantse wajen gudanar da ayyukan da za su bada damar zaunar da zaman lafiya mai dorewa a kasar.

A ranar asabar da ta gabata ne dai a birnin Alger, na kasar Algeria kungiyoyin ‘yan tawayen Arewacin kasar Mali, tare da gwamnati suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, yarjejeniya da ake cike da fatan ganin za ta kawo karshen rikicin da kasar ke fama da shi tun a farkon shekarun 1960.

Faransa dai na daga cikin kasashen da suka tura dimbin sojoji zuwa arewacin Mali a lokacin da rikici ya barke tsakanin gwamnati da  ‘yan tawayen, duk da cewa Faransa ta ce ta shiga kasar ne domin yaki da ‘yan ta’adda.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.