Azbinawa sun sanya hannu kan yarjejeniyar sulhu da gwamnati Mali
A yau asabar manyan kungiyoyin Azbinawa ‘yan tawaye a kasar Mali sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta dindindin da gwmanatin kasar Mali a gaban idon wakilan kasashen duniya.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Yarjejeniyar dai ana fatar za ta kawo karshen tashin hankalin ake fama da shi a yankin arewacin Mali tun bayan samun ‘yancin kan kasar, wanda ya kara tsananta a shekara ta 2012.
Babbar kungiyar ‘yan tawayen CMA, ta amince da daftarin sulhun tun kafin gwamnatin Mali ta sanya masa hannu a ranar 15 ga watan mayu, bayan share tsawon lokaci ana tattaunawa tsakanin bangarorin a birnin Alger na kasar Algeria,
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu