Isa ga babban shafi
Faransa-Mali

Faransa za ta cigaba da kawo taimako zuwa kasar Mali

A yau litinin ministan tsaron Faransa Jean-yves Le Drian, zai kai ziyara a kasar Mali, domin jaddada goyon bayan Faransa ga yarjejeniya zaman lahiya da aka cimma tsakanin yan Tawaye da Gwamnatin kasar. Faransa dai na daga cikin kasashen da suka tura dimbin sojoji zuwa arewacin Mali a lokacin da rikici ya barke tsakanin gwamnati da kuma ‘yan tawayen, duk da cewa Faransa ta ce ta shiga kasar ne domin yaki da ‘yan ta’adda da suka shiga Mali. 

Jean Yves Ledrian ministan Tsaron Faransa
Jean Yves Ledrian ministan Tsaron Faransa RTL
Talla

Kungiyoyin ‘yan tawayen arewacin kasar Mali mafi yawansu Azibinawa da kuma Larabawa, sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da gwmanatin kasar a ranar asabar da ta gabata, an dai shirya wani gagarumin biki a birnin Bamako tare da halartar sugaban kasar Ibrahim Boubakar Keita.
Wannan yarjejeniya ce da ake fatar za ta kawo karshen rikicin da kasar ta Mali ke fama da shi tun bayan samun ‘yancin kai a farkon shekarun 1960, rikicin da yak ara tsananta shekaru 3 da suka gabata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.