Faransa za ta kara yawan tallafin rundunar MDD a Mali
Gwamnatin Kasar Faransa za ta kara yawan tallafin da take bai wa rundunar wanzar da zaman lafiya na Majalisr Dinkin Duniya a Kasar Mali.
Wallafawa ranar:
Ministan tsaron Faransa ne Jean-Yves Le Drian ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da jawabi a garin Gao na arewacin kasar Mali.
A karshen wannan wata ne dai wa’adin aikin rundunar ta Majilisar Dinkin Duniya zai kawo karshe, amma ana fatar kwamitin tsaro na majalisar zai tsawaita wa’adin aikin rundunar, yayin da sojojin Faransa da ke aiki a kasar za su danka wa rundunar wasu daga cikin yankuna da ke karkashin kulawarsu a arewacin Mali bayan sulhun da aka cimma tsakanin gwmanati da ‘Yan tawaye.
Kasar Faransa nada dakaru kimanin 1, 350 da ta aike a matsayin gudun mawarta danagane da yaki da ta'addaci a Mali.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu